in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ra'ayin ministan harkokin wajen kasar Sin kan shawarwari tsakanin Palasdinu da Isra'ila
2013-12-20 16:48:09 cri
Ministan harkokin wajen kasar Sin Mr Wang Yi ya halarci taron masu sha'awar wanzuwar yanayin zaman lafiya tsakanin Palasdinu da Isra'ila, wanda ya gudana ranar Alhamis 19 ga watan a birnin Kudus. Mahalarta taron daga bangarorin biyu, sun bayyana ra'ayoyinsu yadda ya kamata, tare kuma da nuna kyakkyawar fatan samun zaman lafiya a yankin gabas ta tsakiya, da kuma fatan Sin za ta kara taka rawar da ta dace dangane da wannan batu.

Yayin taron, Wang Yi ya nuna cewa, Sin na da aniyar sauke nauyin aikin kiyaye zaman lafiya da karko a sassan duniya baki daya. Kuma tuni, kasar ta Sin ta dora muhimmanci sosai kan wannan batu. A ganinta batun Palasdinu ya kasance muhimmin lamari da aka sa a gaba a yankin gabas ta tsakiya. Mr. Wang ya kara da cewa kasar Sin na yin iyakacin kokarin shimfida yanayin zaman lafiya da karko a wannan yanki.

Ban da haka, Wang Yi ya bayyana cewa, cikin kwanakin nan biyu da suka wuce, ya tattauna da shugabannin kasashen sassan biyu kan batun shawarwari tsakaninsu. Ya ce abin da ya fi jawo hankalinsa shi ne, ko da yake bangarorin biyu na da bambancin ra'ayi, amma a hannu guda dukkansu na bayyana burinsu na ci gaba da gudanar da shawarwari, a matsayin hanya daya tilo ta warware rikicin dake tsakaninsu. Haka zalika suna ganin cewa, za su yi amfani da damarsu wajen sa kaimi ga yin shawarwarin dake tsakaninsu, ta yadda za a laluben hanyoyin daidaituwa, kuma a kaiwa ga cimma matsaya guda a karshe. (Amina)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China