in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An kai hari kan wani gini na MDD a zirin Gaza
2014-07-25 10:09:13 cri
Mataimakin kakakin babban sakataren MDD Farhan Haq ya bayyana a ranar 24 ga wata cewa, a wannan rana an kai hari kan wani gini na MDD dake dauke da 'yan gudun hijira fiye da dari daya a zirin Gaza, lamarin da ya haddasa mutuwar mutane da dama ciki har da ma'aikatan MDD.

Mr. Haq ya ce, babban sakataren MDD Ban Ki-moon ya yi Allah wadai da wannan hari, kana ya jaddada cewa, tilas ne Palesdinu da Isra'ila su martaba dokokin jin kai na duniya.

Bugu da kari, Ban Ki-moon ya ce, harin ya sheda cewa, tilas ne sassan biyu su dakatar da kai wa juna hare-hare ba tare da bata lokaci ba. Shi kuma, a cewarsa, zai ci gaba da yin kokari tare da kasashen duniya da kuma kasashen da ke wannan yanki don sa kaimin ganin bangarorin biyu su tsagaita bude wuta a tsakaninsu cikin hanzari. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China