Mr Wang yayi wannan bayanin ne a wata hira da tashar larabci na kafar yada labarai ta Al Jazeera mai cibiya a Qatar,kamar yadda wata sanarwa da aka fitar daga ofishin sa ta nuna a ranar alhamis din nan 9 ga wata.
Da yake bayani akan matakai hudun Mr Wang yace kasar Sin da farko tana nan a kan bakanta na cewa a dakatar da bude wuta tare da dai na tashin hankali ba tare da bata lokaci ba domin a samar da doka da oda a kasar.
Sai na biyu da ya ce yana da muhimmanci a fara tattaunawar a siyasance nan take domin a samu mafita da dukkan bangarorin dake fada da juna zasu amince da ita.
A mataki na uku inji shi ya kamata kasashen duniya su maida kaimi wajen ganin anyi tattaunawar sulhu, tare da kira ga dukkan bangarorin biyu da su shiga cikin tattaunawar.
Sannan ministan yayi bayani game da matakin karshe na hudu shine a tabbatar da samar da jin kai a Sudan ta Kudu. (Fatimah Jibril)