Bayan da Wang Yi ya sauri matakan da bangarorin biyu suka dauka a halin da ake ciki yanzu. Ya jaddada cewa, Sudan ta Kudu wata sabuwar kasa ce, nauyi mafi muhimmanci da aka dora wa bangarori daban daban na kasar shi ne a tabbatar da zaman lafiya da karko da farfado da tattalin arzikin kasar. Kasar Sin tana fatan bangarorin biyu za su yi la'akari da moriyar jama'ar kasar cikin dogon lokaci, don tsagaita bude wuta nan take, da tabbatar da zaman doka da oda da gaggauta farfado da shawarwari don lalubo bakin zauren warware wannan matsala.
Wang Yi ya ce, ko da yake akwai bambancin ra'ayi a tsakanin bangarorin biyu, amma irin sabanin da ke tsakaninsu yana ta raguwa, kuma an kara cimma ra'ayi guda a tsakaninsu, sun tsaida sharadin yin shawarwari a tsakaninsu, yana fatan bangarorin biyu za su fara yin shawarwari a hukunce, ta yadda za'a iya kawo karshen rikicin zubar da jini.
Bangarorin biyu da rikicin Sudan ta Kudu ya shafa sun jinjina matsayin da kasar Sin ke bi a kai, kuma suna fatan warware rikicin ta hanyar shawarwarin, kuma suna fatan gaggauta yin shawarwari a hukunce. Ban da wannan kuma, bangarorin biyu sun yi maraba da kasar Sin da ta ci gaba da taka muhimmiyar rawa a cikin shawarwarin, kuma sun jaddada cewa ya zama dole a dauki hakikanin matakai don tabbatar da tsaron hukumomin da jama'a a kasar Sudan ta Kudu. (Bako)