A cikin wata sanarwa da aka fitar,kwamitin sun jaddada bukatar da ke akwai tsakanin shugaban kasar Salva Kiir Mayardit da kuma tsohon mataimakin sa Reik Machar da sauran shugabannin siyasa dasu nuna dattaku ta hanyar amincewa da su yi tattaunawar da zai kai ga dakatar da bude wuta nan take.
Kwamitin ya bukaci Machar da ya kara kaimi na ganin ya amince da dakatar da fada daga bangaren magoya bayan sa ba tare da gindaya sharadi ba,sannan kuma suka bukaci gwamnatin sabuwar kasar musamman ma Shugaban kasar Salva Kiir da ya saki dukkannin fursunonin siyasa da ya daure domin a samar da wani yanayi mai kyau da zai kai ga samun zaman lafiya.
Mambobin kwamitin sulhun har ila yau sun bukaci kawo karshen duk wani nau'i na cin zarafin dan adam da take hakkin su, suna masu jaddada za'a tuhumi wadanda suke wannan aika aika da alhakin bisa wuyan su.(Fatimah Jibril)