in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sojojin Sudan ta kudu na kokarin sake kwato garin Bor daga hannun 'yan tawaye
2014-01-04 16:11:56 cri
Rahotanni daga kasar Sudan ta kudu na cewa, sojojin kasar suna kara dannawa zuwa muhimmin garin nan na Bor da 'yan tawayen dake biyayya ga tsohon mataimakin shugaban kasar Riek Macha suka kwace, yayin da aka fara tattaunawa tsakanin sassan biyu ranar Jumma'a a Addis Ababa, babban birnin kasar Habasha.

Dakarun gwamnatin sun samu nasarar fara kutsawa birnin ne, yayin da 'yan tawayen suka amince su fara tattaunawa da nufin cimma yarjejeniyar tsagaita bude wuta tare da kawo karshen tashin hankalin da ya barke ranar 15 ga watan Disamba a wannan jaririyar kasa.

Kafar yada labarun Sudan Tribune ta ruwaito kakakin sojojin Sudan ta kudu Philip Aguer na tabbatar da wannan labarin, kana sojojin sun himmatu wajen ganin sun sake kwato garin Bantio, babban birnin jihar Unity mai arzikin mai da 'yan tawayen ke rike da shi. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China