Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Hong Lei ya shaidawa manema labarai cewa, nasarar dinke barakar cikin gida da Paladinawan suka yi, za ta kara karfafa hadin kan al'ummar Palasdinu a kokarin da suke yi na neman kasar Palasdinu tare da samar da zaman lafiya da fahimtar juna tsakanin Palasdinu da Isra'ila.
Kasar Sin ta yi imanin cewa, sassantawa cikin lumana, ita ce hanya daya tilo ta tabbatar kasancewar kasashen biyu. Kuma tana fatan Isra'ila da Palasdinu za su warware bambance-bambancen da ke tsakaninsu, kana su koma kan teburin sulhu.
Hong Lei ya yi kira ga kasashen duniya da su goyi bayan wannan yunkuri. (Ibrahim)