in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin na fatan kasashen duniya za su samar da kyakkyawan yanayi na yin shawarwarin zaman lafiya a tsakanin Palasdinu da Isra'ila
2013-05-10 17:07:13 cri
Dangane da yabon da kasashen duniya suka nuna kan yadda kasar Sin ta karbi shugabannin kasashen Palasdinu da Isra'ila yayin da suka kawo ziyara a kasar, madam Hua Chunying, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin ta bayyana a ranar 10 ga wata a nan Beijing cewa, karbar shugabannin kasashen 2 a ziyarar da suka kawo nan kasar Sin, wani sabon kokari ne da kasar Sin ke yi domin kara azama kan yin shawarwarin zaman lafiya a tsakanin kasashen 2, hakan ya nuna cewa, kasar Sin na himmantuwa wajen warware batun Palasdinu da sauran batutuwan da ke shafar yankin Gabas ta Tsakiya, wadanda suka jawo hankali sosai, da kuma tabbatar da samun zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin. Kasar Sin na fatan abin da ta yi zai taimaka wajen hada kan kasashen duniya don su samar da kyakkyawan yanayi na yin shawarwarin zaman lafiya a tsakanin Palasdinu da Isra'ila.

Game da sakamakon ziyarar shugabannin Palasdinu da Isra'ila a nan kasar Sin, madam Hua ta ce, a lokacin da suke ziyara a nan kasar Sin, shugabannin kasar Sin sun mai da hankali kan shiga tsakani dangane da batun Palasdinu, inda shugaba Xi Jinping na kasar Sin ya gabatar da ra'ayoyinsa hudu kan warware batun Palasdinu. Ban da wannan kuma, kasar Sin ta yi musayar ra'ayoyi tare da shugabannin kasashen 2 daya bayan daya kan yadda za a raya dangantakar da ke tsakanin Sin da kasashen 2. (Tasallah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China