in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yammacin Afrika na fuskantar matsi sakamakon barkewar cutar Ebola
2014-07-16 13:50:01 cri

Hukumar kiwon lafiya ta duniya (WHO), ta gabatar da rahoto game da barkewar cutar Ebola a yankunan yammacin Afrika.

Rahoton wanda ya fayyace yanayin da ake ciki a yankin, ya nuna yadda yankin na yammancin Afirka ya fada wani mawuyacin hali, sakamakon karin mutane da suke kamuwa da wannan cuta, musamman ma a kasashen Saliyo da Labeliya in da ta fi tsananta.

Rahoton ya ce, daga ranar 8 zuwa 12 ga wannan wata na Yuli, Saliyo ta ba da rahoton karuwar mutane 49 da ake zato ko aka tabbatar sun kamu da cutar, yayin da adadin wadanda suka mutu ya karu da mutum 52.

An ce a Laberiya kadai an samu karuwar mutane 30 da suka kamu da cutar, baya ga karin mutane 13 da suka rasu. Hakan dai na nuna yadda wannan cutar ke dada yaduwa a tsakanin al'umma.

Har wa yau rahoton ya bayyana cewa, yanzu haka ana amfani da cibiyar gudanar da rigakafin cututuka da WHOn ta kafa a birnin Konakry hedkwatar kasar Guinea, inda sashin lura da harkokin Afirka na hukumar ya yanke shawarar tura masana a fannin cututuka, da kimiyyar magunguna zuwa wannan cibiya. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China