Alkalumman baya-bayan nan sun nuna cewar mutane 157 ne suka kamu da cutar ta Ebola a kasar Guinea. Kuma wasu mutane 101 sun rasa rayukansu a sakamakon kamuwa da cutar. Hakazalika ya zuwa jiya Alhamis an tabbatar ta hanyar gwajin kimiyya, kamuwar wadansu mutane 66.
A halin da ake ciki hukumar lafiyar ta duniyar ta bullo da wata hanya ta gane wadanda suka yi mu'amala da wadanda suka kamu da cutar ta Ebola.
Hukumar ta yi hakan ne ta hanyar shirya wani taron karawa juna ilmi domin horas da mutane 70 wadanda ake sa ran za su shiga kauyuka domin gano wadanda suka yi mu'amala da wadanda aka tabbatar suna dauke da cutar ta Ebola.
A halin da ake ciki, hukumar lafiyar ta duniyar za ta kafa wata cibiya a ma'aikatar lafiya ta kasar Guinea wacce za ta dinga bayar da gargadi tare da daukar matakai gaggawa. Cibiyar za ta kuma sa ido wajen gano cutar, aiwatar da bincike tare da samar da uzuri na sufuri, da kwantarwa a asibiti da kuma daukar nauyin wadanda suka kamu da cutar bayan rasuwarsu.
Hukumar lafiyar ta duniya ta jaddada cewa, wayar da kan jama'a a kan daukar matakai na kariya da barazanar cutar, su ne hanyoyi mafi nagarta na hana yaduwar cutar da mutuwar jama'a. (Suwaiba)