Sanarwar ta ce, wasu mutane suna musunta yaduwar cutar Ebola, yayin da wasu kuma suke tsammanin cewa, babu bukata a yi rigakafi ko zuwa likita idan an kuamua da wannan wannan cuta. Bayan haka, sanarwar ta kara da cewa, idan ba za a iyar kawar da tsoro da rashin fahimta kan cutar ba, ta yadda za'a samu fadakar da mutane, to akwai matukar wahala a dakile hanyoyin yaduwar cutar Ebola.(Fatima)