A yayin tattaunawar, jami'an biyu sun maida hankali kan matsalar cutar Ebola ta yi sanadiyyar mutuwar mutane 122 tare da fiye de mutane 190 dake fama da cutar wadanda ke samun jinya a cibiyoyin dake yankunan da annobar ta fi shafa.
Manzon musamman na MDD ya bayyana damuwar MDD kan wannan annoba data shafi kasashe da dama na yammacin Afrika, inda Guinee ta fi samun yawan mutanen da suka mutu a matsayin kasar wannan cuta ta barke.
A matsayin ziyarar gani da ido a yammacin Afrika, akwai muhimmanci waje na in kawo ziyara Guinee dake huldar dangantaka mai karfi tare da MDD in ji mista Feltman kafin ya kara da cewa ziyararsa tana nuna goyon baya ga gwamnati da jama'ar Guinee.
Haka kuma da sunan babban sakatare janar na MDD, mista Feltman ya nuna cewa ziyararsa ta kasance wata dama domin tattaunawa tare shugaban Guinee kan batutuwan siyasa, musamman kan girmama yarjejeniyoyin siyasar fita daga rikici da aka rattaba wa hannu a cikin watan Yulin shekarar 2013 tsakanin bangarorin siyasar kasar Guinee da kuma kafa sabuwar majalisar dokoki. (Maman Ada)