Bisa kididdigar, kasar Guinea ta fi sauran kasashe yawan masu cutar ta Ebola, inda mutane 413 suka kamu da ita, cikinsu 303 sun rasa rayukansu. A kasar Liberia, akwai mutane 107 da suka kamu da cutar, kuma 65 a cikinsu sun mutu. Sai kuma kasar Saliyo, inda mutane 99 a cikin masu fama da cutar 239 suka mutu. An ce, yawan mutane da suka kamu da cutar da wadanda suka mutu a sakamakon kamu da cutar ya kai matsayin koli a tarihi.
Don hana yaduwar cutar ta Ebola, ministocin kiwon lafiya na kasashen yammacin Afirka 11 za su gudanar da wani taron gaggawa a Accra dake kasar Ghana a ranakun 2 da 3 ga watan nan, inda za su tsara shirin hadin gwiwar kasa da kasa wajen tinkarar cutar. (Zainab)