A shafin yanar gizon hukumar da aka buga a ranar alhamis din nan an ce wadanda suka mutu sakamakon cutar sun karu daga 121 zuwa 137 a cikin kwanaki ukku, inda yawancin wadanda suka mutu a kwanakin baya, ko kuma kashi 87% daga cikinsu, 'yan kasar Guinea ne.
Adadin wadanda ake zargi da wadanda aka tabbatar da kamuwa da cutar a Guinea,da Liberiya da kuma Saliyo sun haura daga 194 zuwa 236 a cikin kwanaki ukku da suka wuce. Wanda yawancin sabbin masu dauke da cutar sun fito ne daga kasashen Guinean da kuma Saliyo. (Fatimah Jibril)