Ma'aikatar kiwon lafiya ta kasar Liberiya ta bayar da wata sanarwa a ranar 30 ga watan Yuni cewa, a cikin mutane 90 da aka tabbatar da cewa sun kamu da cutar Ebola a kasar, mutane 49 daga cikinsu sun riga sun mutu.
Sanarwar ta ce, mutanen 49 da suka mutu sun hada da ma'aikatan likitoci 5. Haka kuma, sanarwar ta kara da cewa, a halin yanzu dai mutane 441 aka tabbatar sun yi mu'amala da masu kamu da wannan cuta a kasar, haka kuma an riga an kebe wasu 419 daga cikinsu a cikin asibiti domin bincikensu.
A farkon watan Fabrairu na shekarar bana, yankunan dake kudu maso gabashin kasar Guinea sun gamu da barkewar cutar Ebola, sa'an nan kuma cutar ta yadu zuwa kasashen da ke makwabtaka da ita ciki har da Liberia cikin sauri. A farkon watan Afrilu, an dan dakatar da yaduwarta, amma bayan haka cutar ta sake yaduwa cikin sauri. Hukumar kiwon lafiya ta WHO ta taba yin bayani cewa, yanayin yaduwar wannan cutar a yammacin Afirka ya fi wanda aka taba samu a baya tsanani. (Danladi)