Sanarwar ta bayyana cewa, ganin yadda ake cigaba da samun karuwar mutanen da suka mutu sakamakon cutar Ebola a kasar Guinea, kungiyar ba da agaji ta Red Cross da Red Crescent ta yi kira da a tara kudin tallafi na dala miliyan 1.4, domin kawar da kwayoyin cuta, hana yaduwarta tsakanin mutane da sanya ido ga mutanen da suka taba zama kusa da masu jinya, kyautata tsarin jinya a yankunan karkara, da dai sauransu.(Bello Wang)