in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yawan mutanen da cutar Ebola ta hallaka ya kai 72 a Guinea
2014-04-27 16:01:38 cri
Rahotannin baya-bayan nan daga kasar Guinea na cewa, daga watan Janairun bana kawo wannan lokaci, yawan mutanen da cutar Ebola ta hallaka a kasar ya kai mutum 72.

Ma'aikatar lafiyar kasar wadda ta tabbatar da hakan ta ce, adadin mamatan ya karu daga 61 da aka bayyana a baya.

Da yake karin haske game da hakan, wani jami'in ma'aikatar lafiyar kasar Sakoba Keita, ya ce a ranar Jumma'ar da ta gabata, tawagar jami'an lafiya dake aikin dakile yaduwar cutar sun bayyana cewa, jimillar mutanen da aka tabbatar sun kamu da cutar ta Ebola sun kai mutum 115.

Kazalika a ranar Alhamis hukumar lafiya ta duniya WHO ta ce adadin wadanda suka rasu sakamakon kamuwa da wannan cuta a kasashen yammacin Afirka ya kai mutum 147, yayin da a kasashen Guinea da Liberia kadai adadin wadanda aka tabbatar sun kamu da cutar ya kai mutum 240.

WHO dai ta bayyana cutar Ebola a mastayin daya daga muggan cutuka masu saurin hallaka bil'adama a ban kasa.

An kuma fara samun barkewar cutar ne cikin shekarar 1976 a kasashen Sudan da jamhuriyar dimokaradiyyar Congo. Kuma kawo yanzu wannnan cuta ba ta da magani, ko wani cikakken rigakafi.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China