Yayin da yake magana da 'yan jarida, Keiji Fukuda ya bayyana cewa, yanzu cutar Ebola dake yaduwa a kasashen Guinea da Liberia da kuma Sierra LeoneSaliyo na ci gaba da yaduwa, amma ana iya kulawa da ita, Sannan sannan kuma ana cikin wani yanayi mai kyau na yin rigakafi da kuma yaki da ita. A sa'i daya kuma, ya yaba a kan jerin matakan da gwamnatin Guinea ta dauka bayan barkewar cutar Ebola, wato kara sa ido, ba da jiyya da kebe wadanda suka kamu da cutar zuwa wuri na daban, da kafa dakin gwaji, da kara karfin fadakarwa da sauransu.
Feiji Fukuda ya je birnin Konakry ne bayan da ya halarci taron gaggawa na ministocin kasashen yammacin Afirka da aka shirya a birnin Accra, hedkwatar Ghana a ranar 2 ga wata.(Fatima)