A kwanakin baya, don magance yiwuwar samun cutar Ebola a kasar Cote d'Ivoire, ma'aikatar kiwon lafiya ta kasar ta bada umurnin kara daukar matakan sa ido kan cutar, da hana jama'ar kasar su ci namun daji, da kara sa ido kan mutane dake zirga-zirga a yankin iyakar kasa a tsakaninta da kasashen Guinea, Liberia da Saliyo wadanda aka samu cutar Ebola a cikinsu. Ya zuwa yanzu, ba a gano ko wane mutum da ya kamu da cutar Ebola a kasar ta Cote d' Ivoire ba.
Bisa kididdigar da hukumar kiwon lafiya ta duniya wato WHO ta yi, an ce, ya zuwa ranar 8 ga watan Yuli, mutane 888 a kasashen Guinea, Liberia da Saliyo sun kamu da cutar Ebola ko ake zargin su da kamuwa da shi, guda 539 a cikinsu sun rasa rayukansu. (Zainab)