Ministar kiwon lafiya ta kasar Saliyo Madam Miatta Kargbo ta bayyana a ranar 30 ga watan Yuni cewa, hukumar shirin abinci ta MDD ta riga ta bayar da taimakon abinci don taimakawa kasar Saliyo wajen yaki da cutar Ebola.
Yayin da take zantawa da manema labaru, Madam Kargbo ta ce, kayayyakin da hukumar ta bai wa kasar sun hada da mai na dafa abinci, wake, shimkafa da dai sauransu, kuma wadannan kayayyakin cimaka za su isa ga iyalan dake yankunan da suka fi fama da cutar Ebola, wadanda suka rasa wasu mambobinsu sakamakon cutar.
Bisa kididdigar da Madam Kargbo ta bayar, an ce, ya zuwa yanzu mutane 188 a kasar sun kamu da cutar Ebola, cikinsu wasu 56 sun mutu, yayin da wasu 22 suka warke. (Danladi)