Kakakin ma'aikatar tsaron kasar Sin Mista Yang Yujun ya bayyana a ran 28 ga wata cewa, zirga-zirgar jiragen sama a yankin da aka shata na tsaron sararin samaniya na tekun Gabas na kasar Sin ba a kawo wani illa ba, yana fatan bangarorin da abin ya shafa su hada kai da kasar Sin, domin tabbatar da zirga-zirgar jiragen sama yadda ya kamata.
Bayan da kasar Sin ta sanar da shata yankin tsaron sararin samaniya a tekun Gabas, bisa bukatar gwamnatin kasar Japan, kamfanonin jiragen sama biyu na Japan da suka yi niyyar mika bukatarsu ga kasar Sin na bin wannan hanya, sun canza ra'ayinsu inda suka sanar da cewa, ba za su gabatar da bayanai na zirga-zirgarsu ba ga kasar Sin.
A nata banagren, ita ma kasar Amurka ta ce, tana nazari kan ko za ta gabatar da shirin zirga-zirgarta ga kasar Sin ko a'a.
Game da haka, Mista Yang ya bayyana a taron manema labaru da da aka shirya a ko wane wata cewa, sanarwar shata yankin tsaro a sararin samaniya a tekun gabas na kasar Sin ta riga ta tanadi cikakken bayani kan na'urorin da ke tafiya a sararin samaniya, wannan dai ya dace da dokar kasa da kasa.(Danladi)