Cui Tiankai ya ce, tsibirin Diaoyu da sauran kananan tsibiran dake kusa da shi sun kasance cikin yankin kasar Sin tun fil azal, saboda haka kasar Sin ba zata taba sauya ra'ayinta ba kan mallakar tsibirin, wanda a ganinta bai kamata a rika tuhumar hakan ba. Yayin da kasashen Sin da Japan suka yi kokarin kyautata huldar dake tsakaninsu, shugabannin kasashen 2 sun tsai da cewa za'a dakatar da ja'in ja a kan wannan batu. Sai dai tabarbarewar yanayin da aka shiga yanzu an same shi ne sakamakon aikace-aikacen kasar Japan.
Haka kuma a lokacin da ya tabo maganar zirin Koriya, Cui ya ce, kasar Sin tana tsayawa kan manufofi 3, wato da farko, tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a zirin Koriya. Na biyu, kokarin kau da makaman nukiliya a zirin. Sannan na uku ita ce, tsayawa kan hanyar tattaunawa don warware rikici. Wadannan manufofi 3 suna da alaka da juna, don haka kada a raba su. Kasar Sin, a nata bangaren, za ta ci gaba da kokari ganin an wanzar da zaman lafiya a zirin Koroya da kau da makaman nukiliya daga zirin. (Bello Wang)