Bisa labarin da aka bayar, an ce, gwamnatin kasar Japan ta tabbatar da shirinta na kakkabo jiragen saman da babu matuka da suka shiga sararin saman kasarta ba izni ba, ciki har da matakin harbo duk wasu jiragen saman da suke keta yankinta. A kwanakin baya, firaministan kasar Japan Shinzo Abe ya saurari rahoto game da wannan shiri, kuma ya amince da shi.
Game da wannan batu, Hua ta ce, kasar Japan ta ba da labari dangane da barazana daga kasashen waje, da yin amfani da wannan dalili don ta da zaune tsaye da kuma kara jibge makamai, kasa da kasa sun nuna damuwa sosai ga hakikanin yunkurinta.
Ban da wannan kuma, Hua ta jaddada cewa, tsibirin Diaoyu yankin kasar Sin ne, kasar Sin tana da karfi wajen tabbatar da ikon mallakar yankinta, kuma za ta tinkari duk wani ta da zaune tsaye da kasashen waje za su yi mata. (Zainab)