Ran 15 ga wata, yayin da yake amsa tambayoyin manema labarai game da ziyarar ban girma da wasu jami'an gwamnatin kasar Japan suka kai a haikalin Yasukuni, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Hong Lei ya bayyana cewa, a wannan rana da safe, mataimakin ministan ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Liu Zhenmin ya riga ya gana da jakadan kasar Japan da ke kasar Sin cikin gaggawa, inda ya yi suka mai tsanani dangane da lamarin.
Hong Lei ya kuma kara da cewa, lamarin ya bata ran jama'ar kasar Sin da sauran jama'ar kasashen Asiya wadanda suka shiga yakin duniya na biyu, domin wasu jami'an kasar Japan sun kai ziyarar ban girma ga wadanda suka aikata laifuffuka a haikalin Yasukuni.
Ya kuma sake jaddada cewa, ya kamata kasar Japan ta amince da laifuffukan da ta aikata a baya cikin tarihi, ta kuma yi gyara, ta yadda za ta iya neman ci gaba da samun kaykayawar makoma. Kasar Sin ta yi kira ga kasar Japan da ta dauki matakai yadda ya kamata don neman amincewar gamayyar kasa da kasa, in ko ba haka ba, kasashe masu makwabta ba za su yi hakuri da ita ba. (Maryam)