in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasa da kashi 10 bisa dari na makamai masu guba ba'a fitar da su daga kasar Sham ba
2014-04-28 10:51:13 cri

Kungiyar haramta makamai masu guba ta bayyana a ran 27 ga wata cewa, kasa da kashi 10 bisa dari na makamai masu guba na kasar Sham ba a fitar da su daga kasar Sham ba.

Wakiliyar musamman ta tawagar hadin gwiwa ta kungiyar haramta makamai masu guba ta MDD Madam Sigrid Kaag ta yi wannan furuci ne a yayin wani taron manema labaru da aka shirya a birnin Damascus, inda ta bayyana cewa, a halin yanzu dai kashi 7.5 zuwa 8 bisa dari na makamai masu guba da gwamnatin Sham ta yi rajista ba a jigilar da su zuwa ketare ba tukuna. Sakamakon rashin tsaro, tawagarta ba za ta iyar gudanar da aikinta ba a wuraren da aka ajiye wadannan makamai dalilin rashin tsaro.

Kaag ta ci gaba da cewa, game da sauran wadannan makaman da aka ambato, ya kamata a yi jigilar kashi 75 bisa dari zuwa ketare, sauransu kuma za a lalata su a wurin da aka ajiye su.

Wannan shi ne karo na biyu da aka wuce wa'adin da aka kayyade dangane da aikin jigilar da makamai masu guba daga kasar Sham zuwa ketare. (Danladi)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China