Kakakin babban sakataren MDD Stephane Dujarric ya bayyana a ran 21 ga wata cewa, kashi 80 bisa dari na makamai masu guba na kasar Sham an riga an yi jigilarsu zuwa kasashen waje, wasu kuma an lalata su.
Dujarric ya yi wannan bayani ne a gun taron manema labaru da aka shirya a hedkwatar MDD da ke birnin New York, inda ya yi nuni cewa, mai samun sulhuntawa na musamman daga tawagar hadin kan kungiyar haramta makamai masu guba da MDD, Madam Sigrid Kaag ta bayar da wata sanarwa a karshen makon jiya cewa, bayan da aka yi jigilar Karin wasu kayayyakin makamai masu guba daga tashar ruwa ta Sham zuwa ketare, an riga an yi jigilar kashi 80 bisa dari na kayayyakin makamashi masu guba wasu kuma aka lalata su a cikin kasar. A sakamakon aikin da ake gudanarwa a halin yanzu, Sham za ta iya gama aikinta kafin wa'adin karshe da kungiyar haramta makamai masu guba ta tsaida wajen jigilar kayayyakin zuwa ketare ko kuma lalata su a gida. (Danladi)