in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta nuna damuwa game da yanayin da Isra'ila da Falesdinu suke ciki
2014-07-02 20:15:45 cri
A jiya Talata 1 ga wata ne, sojojin Isra'ila suka harba boma-bomai kan yankin Gaza dake karkashin ikon kungiyar Hamas. Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya bayyana cewa, kasarsa za ta kara daukar matakan soja kan Hamas idan har bukatar hakan ta taso.

Dangane da lamarin, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Hong Lei ya bayyana a yau Laraba 2 ga wata cewa, Sin na damuwa sosai da yadda ricikin dake tsakanin Isra'ila da Falesdinu ke ci gaba da karuwa, don haka ta sake yin kira ga bangarorin da abin ya shafa da su dukufa wajen kai zuciya nesa. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China