in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin tana fatan Falesdinu da Isra'ila za su cimma matsaya guda ba tare da jinkiri ba
2013-07-24 10:52:44 cri
A ranar 23 ga wata, mataimakin zaunannen wakilin kasar Sin a M.D.D. Wang Min ya bayyana cewa, kasar Sin tana maraba da farfado da shawarwari tsakanin Falesdinu da Isra'ila, kuma tana fatan bangarorin biyu za su haye wahalhalu da ke gabansu, da inganta hadin gwiwa, don gaggauta cimma matsaya guda ba tare da wani bata lokaci ba.

A gun wani taron da kwamitin sulhu na M.D.D. ya shirya game da batun Gabas ta tsakiya, Wang Min ya bayyana cewa, hanya daya tak da za a bi wajen warware rikicin da ke tsakanin Falesdinu da Isra'ila ita ce, yin shawarwari tsakaninsu. Kasar Sin ta yaba wa kokari da bangarorin daban daban da wannan batu ya shafa ke yi, kuma tana fatan Falesdinu da Isra'ila su shawo kan matsalolin da ke gabansu, su kuma gaggauta cimma matsaya guda tsakaninsu.

Wang Min ya ci gaba da bayyana cewa, kasar Sin tana goyon bayan M.D.D, musamman ma kwamitin sulhu na M.D.D. don gane da muhimmiyar rawa da ya takawa wajen ingiza kasashen duniya ci gaba da nuna goyon baya game da aikin samar da zaman lafiya a yankin Gabas ta tsakiya.(Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China