in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Firaministan kasar Isra'ila ya yi kira ga Falesdinu da ta yi rangwame cikin shawarwarin
2013-11-18 10:15:58 cri
A ranar 17 ga wata, firaministan kasar Isra'ila Benjamin Netanyahu ya jaddada cewa, ba a daina shawarwari da Falesdinu ba, sai dai ya yi kira ga Falesdinu da ta yi rangwame a wurin.

A wannan rana cikin wani hira da ya yi da gidan telebijin CNN, Mr Netanyahu ya ce, ba a daina shawarwari da Falesdinu ba, ana ci gaba da hakan. Sai dai kuma, yana fatan ganin Falesdinu ta dauki wani mataki. Sabo da kowa na cewa ya kamata Isra'ila ta yi rangwame, amma yanzu, lokaci ya yi da Falesdinu ita ma ta yi rangwame, wato ta amince da kasar Yahudawa.

Bayan da Amurka ta yi kokari, tun daga karshen watan Yuli, an farfado da shawarwari kai tsaye tsakanin Isra'ila da Falesdinu, yanzu haka ana kokarin daddale wata yarjejeniya cikin watanni 9 masu zuwa. Sai dai ba a cimma daidaito ba tukuna, saboda Falesdinu tana zargin Isra'ila cewa tana gina matsugunan Yahudawa ne don kawo cikas ga yunkurin samar da zaman lafiya, kana kuma, a farkon wannan wata, rukunin tattaunawa na Falesdinu ya bayyana yin murabus cikin tarayya don nuna adawa ga batun.(Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China