in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta yi maraba ga ci gaban da Falesdinu ta samu wajen cimma daidaito a gida
2014-04-25 20:47:38 cri
kasar Sin ta yi maraba da daidaito da manyan jam'iyyu guda biyu na Falesdinu suka cimma wajen kafuwar hadaddiyar gwamnatin kasa,abin da ta ce zai taimaka wajen karfafa hadin gwiwar jama'ar Falesdinu da kafa kasar cikin 'yancin kai da kuma shimfida zaman lafiya a tsakanin Isra'ila da Falesdinu.

kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Qin Gang ya bayyana hakan yayin taron manema labaran da aka yi a yau Alhamis 24 ga wata, a nan birnin Beijing

Mr Qing Gang ya yi bayanin cewa, kasar ta yi amanna da cewa hanyar shawarwari ita ce hanyar kadai da za ta iya shimfida zaman lafiya a tsakanin Falesdinu da Isra'ila, don haka ya kamata gamayyar kasa da kasa su goyi bayan hakan tare da ci gaba da taimakawa a kan lamarin. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China