Kakakin ma'aikatar harkokin wajen Amurka Jen Psaki ya ba da sanarwa cewa, a wannan rana, sakataren harkokin wajen kasar John Forbes Kerry ya buga waya ga firaministan kasar Isra'ila Benjamin Netanyahu da shugaban hukumar Falesdinu Mahmoud Abbas, inda ya neme su aikawa da kungiyoyin manyan wakilan shawarwari nasu zuwa birnin Washington don komawa teburin shawarwari na kai tsaye.
Ministan kula da harkokin shari'a kuma wakilin shawarwari na farko na Isra'ila Tzipi Livni da manzon musamman na Netanyahu Yitzhak Molcho, da wakilin shawarwari na farko na Falesdinu Saeb Erekat da babban jami'in kasar Mohammad Shtayyeh za su halarci shawarwari na farko da za a fara daga ranar 29 ga wata da dare, don tsara shirin tattaunawa kan batun tabbatar da matsayi na karshe da za a shirya cikin watanni da dama masu zuwa.
A ranar 28 ga wata, majalisar ministoci ta Isra'ila ta jefa kuri'u, don yanke shawarar sakin 'yan fursunoni Falesdinawa 104 da aka tsare a gidan yarin kasar, haka kuma, sakin 'yan fursononi ya zama daya daga cikin sharuda 3 da Falesdinu ta gindaya, don farfado da shawarwari tsakaninta da Isra'ila.(Bako)