Kerry da mashawarcinsa na musamman John R. Allen da daidai ne suka gana da firaministan kasar Isra'ila Benjamin Netanyahu da shugaban Falesdinu Mahmoud Abbas a birnin Kudus da Ramallah, kuma sun bayyyana sabon shirin samar da zaman lafiya gare su, wanda ya kunshi musayar yankunan kasa da batun hedkwatoci na kasashen biyu da sauransu.
Tuni, a wannan rana, wasu jami'an gwamnatin Isra'ila ciki har da Netanyahu suka fada wa kafofin yada labaru cewa, Isra'ila na bukatar tsaron kanta, kuma ba za ta yi sassauci game da batun tsaro a lokacin shawarwarin ba.
Bisa labarin da aka bayar, an ce. Isra'ila za ta tsaya tsayin daka game da kasancewar sojojinta a iyakokin dake tsakaninta da kasar Jordan, don ba da tabbaci ga tsaron iyakokin kasar, kuma tana fatan kafa wuraren tsinkaya a wasu yankunan yammacin gabar kogin Jordan.(Bako)