in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta nuna goyon bayin kasashen duniya da su kara kokarin farfado da shawarwari tsakanin Falesdinu da Isra'ila
2013-06-04 16:54:58 cri
Game da ziyarar sakataren harkokin wajen kasar Amurka John Forbes Kerry a yankin Gabas ta tsakiya, a ranar 4 ga wata, a nan birnin Beijing, yayin da kakakin ma'aikatar kula da harkokin wajen kasar Sin Hong Lei ke zantawa da manema labaru, ya bayyana cewa, kasar Sin ta nuna goyon baya ga bangarorin da abin ya shafa na kasashen duniya da su kara kokarin wajen ingiza cimma burin farfado da shawarwari tsakanin Falesdinu da Isra'ila.

Hong Lei ya ce, Sin ta kan tashi tsaye don nuna goyon baya ga yunkurin samar da zaman lafiya a yankin Gabas ta tsakiya, kwanan baya, shugabannin Falesdinu da Isra'ila sun kawo ziyara kasar Sin daya bayan daya, inda suka bayar da shawarwari 4 game da yadda za a a warware batun Falesdinu. Yanzu, manzon musamman na kasar Sin game da batun yankin Gabas ta tsakiya na yin ziyara a kasashen Masar da Jordan da sauran kasashe. Kasar Sin za ta ci gaba da dukufa ka'in da na'in wajen sa kaimi ga yin shawarwari, don kara yin kokari wajen warware batun Falesdinu cikin daidaito daga dukkan fannoni.(Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China