Ana sa ran kasashen duniya za su sa kaimi game da samar da zaman lafiya tsakanin Falesdinu da Isra'ila
A ranar 5 ga wata, a nan birnin Beijing, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Hong Lei ya sanar da cewa, bisa bukatun da kwamitin kare hakkin Falesdinawa na M.D.D. ya gabatar, an ce, daga ranar 18 zuwa ranar 19 ga wata, gwamnatin Sin za ta dauki nauyin shirya taron kasa da kasa na M.D.D. game da samar da zaman lafiya tsakanin Falesdinu da Isra'ila, kuma kasar Sin tana sa ran taron zai jawo hankalin kasashen duniya game da batun Falesdinu, don sa kaimi ga samar da zaman lafiya game da batun.
Hong Lei ya bayyana cewa, a lokacin, za a gayyaci wakilai na gwamnatocin kasashen duniya da na M.D.D. da na sauran kungiyoyin kasa da kasa da kwararru da masana don halartar taron.(Bako)