Wang Min, wanda ya bayyana hakan a gun taron muhawara game da batun Gabas ta tsakiya, da kwamitin sulhu na M.D.D. ya shirya, ya ce kasar Sin kullum tana dauka cewa, ya kamata Falesdinu da Isra'ila su yi shawarwari a tsakaninsu don cimma burin kafa kasar Falesdinu mai cikakken ikon cin gashin kan ta, kuma mai hedkwata a gabashin birnin Kudus, bisa kuma iyakokin da aka shata a tsakaninta da Isra'ila a shekarar 1967, da tabbatar da zaman tare cikin lumana tsakanin kasashen biyu.
Ya ce, hakan na iya samuwa muddin aka nuna biyayya ga kudurorin da abin ya shafa na M.D.D., da ka'idar "mai da yankunan kasa domin samun zaman lafiya", da "shawarar wanzar da zaman lafiya ta kasashen Larabawa", da kuma "tsarin taswirar" shimfida zaman lafiya a yankin Gabas ta tsakiya.
Wang Min ya kara da cewa, kasar Sin tana fatan yin kokari tare da kasashen duniya, don ba da gudummawa wajen warware batun Falesdinu daga dukkan fannoni kuma cikin adalci, da samun dauwamammen zaman lafiya a yankin Gabas ta tsakiya.
Ya ce, yanzu, aikin farfado da shawarwari kai tsaye tsakanin Falesdinu da Isra'ila, da yunkurin samar da zaman lafiya a yankin Gabas ta tsakiya na samun gagarumin goyon baya, ya kuma yi fatan Falesdinu da Isra'ila za su yi amfani da wannan dama, wajen yin hadin gwiwa, don hana tabarbarewar yunkurin samar da zaman lafiya a tsakaninsu, tare da fatan za su gaggauta samun ci gaba a shawarwarin da suke gudanarwa.(Bako)