A gun bikin ban kwana da aka shirya ga wadannan dalibai, Gong Jianzhong ya ce, hadin gwiwa a fannin ilmi ya zama wani muhimmin bangare na dangantakar hadin gwiwa da ke tsakanin kasashen Sin da Ghana, kuma kasar Sin tana fatan taimakawa kasar Ghana don ta samu bunkasuwa, ta hanyar horar da kwararru, da samar mata da fasahohi. Jakadan Gong ya yi fatan daliban kasar Ghana za su amfani wannan dama ta karatu a kasar Sin, su kuma kammala karatu cikin tsanaki, tare da kara fahimtar zamantakewar al'umma ta kasar, bayan da suka koma gida. Har ila yau ya yi fatan za su yi kokarin raya zamantakewar al'umma, da tattalin arzikin kasar ta Ghana, da kara sada zumunta ta gargajiya a tsakanin kasashen biyu.
A cikin jawabin da matar shugaban kasar Ghana Lordina Mahama ta yi, ta bayyana cewa, kasashen Ghana da Sin, na da dankon zumunci a tsakaninsu, a tsohon lokaci. Ta ce, kasar Sin ta taimakawa kasar Ghana wajen samar da muhimman ababen more rayuwa, da fannin ilmi, da kimiyya da fasaha da sauranu. Ta kuma yi kira ga daliban kasar ta Ghana, da su kiyaye dokokin kasar Sin, da girmama al'adun kasar, don kara ba da gudummawa wajen inganta hadin gwiwa da ke tsakanin kasashen biyu.(Bako)