Arthur ya kuma yin kira ga bangaren da abin ya shafa da su kiyaye zaman lafiya na kasar, a kaucewa jawabin da zai haifar da tashe-tashen hankali.
Bayan babban zaben da aka gudanar a cikin watan Disamban bara a kasar Ghana, hukumar zabe ta sanar da cewa, shugaba mai ci na lokacin, John Dramani Mahama ya ci zaben, sai dai babbar jam'iyyar hamayya ta kasar NPP ta ce, an tabka magudi tare da watsi sakamakon wannan zabe, kuma ta kai kara ga babbar kotun kasar. Babbar kotun kasar ta yanke shawara cewa, a ranar 7 ga watan Agusta, za a yi wani zaman bahasi, inda kuma ake hasashen cewa, za a yanke hukunci na karshe nan ba da dadewa ba.(Bako)