A wannan rana, yayin da yake yin shawarwari da jakadan Sin a Ghana, da kuma membobin rukunin aikin Sin, shugaba Amissah-Arthur ya ce, hakar ma'adinin zinari ba bisa doka ba, ba ma kawai keta dokokin kasar Ghana ba ne, yin hakan na gurbata yankin gona, ruwa, da kuma muhalli.
Ya ce Ghana za ta ci gaba da kokari domin kawar da wannan danyen aiki daga dukkan yankunan kasar. Ya jaddada cewa, ana daukar matakai kan duk wadanda suka keta doka, ciki harda mutanen Ghana da ma 'yan ketare.
Jakadan Sin a Ghana, Gong Jianzhong ya bayyana cewa, gwamnatin Sin ta dora muhimmanci sosai kan batun hakar ma'adinin zinari da Sinawa suka yi a Ghana, tare da nuna fahimta da kuma girmama matakan da kasar ta dauka bisa dokoki, kuma za ta sake tura rukunin ma'aikata zuwa Ghana domin daidaita wannan batu.
Ya zuwa yanzu, bangarorin biyu suna hadin gwiwa tsakaninsu, domin daidaita batun yadda ya kamata. Sin ta bukaci Ghana da ta gudanar da aiki bisa doka ba tare da nuna karfi ba, da tabbatar da tsaro da hakkin Sinawa a kasar.
Sin na fatan yin kokari tare da kasar Ghana, domin daidaita batun hakar ma'adinin zinari ba bisa doka ba yadda ya kamata, a cewar jakadan.
A wannan rana, ofishin jakadancin Sin a Ghana ya shawarci Sinawa masu hakar ma'adinin zinari a Ghana da za su komo kasar Sin, su bi dokokin Ghana, su kuma sayi tikitin jirgin sama tun da wuri, tare da hadin gwiwa da taimakawa juna, a kokarin janyewa daga kasar, tare da kiyaye hakki da moriyarsu. (Fatima)