in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Matakin yaki da aikin hakar zinariya ba bisa doka ba da kasar Ghana ta dauka ba kan Sinawa ne kawai ba, in ji mataimakin shugaban kasar
2013-06-13 14:48:43 cri

Mataimakin shugaban kasar Ghana Kwesi Bekoe Amissah-Arthur ya yi nuni a ran 12 ga wata cewa, matakin yaki da aikin hakar zinariya ba bisa doka ba da Ghana ta dauka ba kan Sinawa kawai ba ne.

A gun taron koli na sha'anin ma'addinai na shekarar 2013 da aka yi a wannan rana a kasar Ghana, Kwesi Bekoe Amissah-Arthur ya yi nuni da cewa, a shekarun baya, 'yan kasashen ketare da dama suna shiga aikin hakar zinariya ba bisa doka ba, inda hakan kan gurbatar muhalli, ruwan sha da gonaki. Hakan ya sa, gwamnatin kasar Ghana ta dauki matakai domin mayar da martani ga duk wanda ya aikata wannan laifi, ciki hadda 'yan kasar Ghana da 'yan kasashen ketare, ta yadda za ta kafa wani tsarin da ya dace wajen gudanar da harkokin kananen wuraren hakar zinariya a wannan fanni, don kawo moriya ga 'yan kasar Ghana.

A wannan rana kuma, yayin ganawa da ya yi tsakaninsa da tawagar hadin gwiwa ta ma'aikatar harkokin waje ta kasar Sin, ma'aikatar cinikayya da ma'aiktar tsaron jama'a ta kasar Sin, minista mai kula da harkokin cikin gida na kasar Ghana Kwesi Ahwoi ya bayyana cewa, Sin da Ghana na da dankon zumunci na dogon lokaci, wannan mataki da Ghana ta dauka ba kan Sinawa kawai ba ne, mataki ne da zummar mayar da martani ga 'yan kasashen ketare da kuma 'yan kasar Ghana masu sabawa doka gaba daya. Ghana na maraba da Sinawa da su zuba jari a kasar ta hanyar da ta dace, kasar Ghana kuma za ta samar da yanayi mai kyau gare su. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China