A hirar sa da wakilin kamfanin dillancin labaru na Xinhua, wani jami'in watsa labarai na hukumar shige da fice ta Ghana ya ce,an cafke mafi yawan mutanen a jihohin dake gabashi da yammacin kasar Ghana. Bisa labarin da kafofin yada labaru na wurin suka bayar, an ce, a cikinsu akwai 'yan Nijer 41, da 'yan Rasha 6, da 'yan Togo 2, da kuma dan Nijeriya guda.
Wannan jami'i ya kara da cewa, bayan da aka yi bincike kan wannan batu, za a tasa keyar wadanda suka keta dokoki zuwa kasarsu.
Ban da haka, a wannan rana kuma, ofishin jakadancin Sin a Ghana ya tabbatar da cewa, Sinawa 158 na jeri na biyu da ake tuhumarsu da hakar ma'adinin zinari ba bisa doka ba a Ghana sun janye daga yankin hakar ma'adinai bisa taimakon ofishin jakadancin Sin a kasar, kuma za su koma gida Sin nan ba da dadewa ba.(Fatima)