A wannan rana, mambobin rukunin sun gana da shugabannin hukumar tsaron kasa da ta shige da fice ta Ghana, inda suka yi shawarwari kan batun yaki da hakar ma'adinin zinari ba bisa doka ba a wurin da kiyaye iko da moriyar Sinawa a wurin da sauransu.
Rukunin ya ce, gwamnatin Sin ta fahimta tare da girmama aikin da Ghana ta yi na yaki da hakar ma'adinin zinari ba bisa doka ba, da fatan daukar kwararran matakai tare da Ghana, a kokarin daidaita matsaloli yadda ya kamata. A don haka Sin ta bukaci Ghana da ta gudanar da bincike bisa dokoki yadda ya kamata, da dakatar da kame Sinawa a waje da yankunan hakar ma'adinai, da dakatar da ayyukan harin da wasu mutanen wurin suke kai wa Sinawan tare da kwace masu dukiyoyi, da kuma tabbatar da tsaron Sinawa da suke son komawa gida Sin, da kiyaye na'urori da sauran dukiyoyin Sinawa bisa iyakacin kokari da sauransu.
Wani jami'in gwamnatin Ghana ya ce, kasar na fatan karfafa mu'amala da hadin gwiwa tsakanin ta da kasar Sin, a kokarin daidaita batun yadda ya kamata. Kuma kasar za ta yi kokarin biyan bukatun Sin a fannoni daban daban.(Fatima)