in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ghana ta gyara dokar zuba jarin waje cikin kananan kasuwannin kasar
2013-07-24 10:47:35 cri
Bisa labarin da kamfanin dillancin labaru na Ghana ya bayar, an ce, kwanan baya, majalisar dokokin kasar ta zartas da gyararriyar doka, game da batun saka jari a kasar, don maye gurbin makamanciyarta da aka zartas a shekarar 1994.

Idan aka kwatanta tsohuwar dokar saka jarin da ta yanzu, gyararriyar dokar ta daga matsayin yawan jarin da kamfanoni masu saka jari za su iya mallaka, kafin su shiga kananan kasuwannin kasar, inda aka baiwa kamfanoni masu zaman kansu da ke da niyyar shiga kananan kasuwannin kasar damar yin rajistar muddin jarinsu ya kai dalar Amurka miliyan guda, maimakon dubu 300 da a da aka amince da shi.(Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China