A ran 14 ga wata, sojojin gwamnatin kasar Sham sun sake kwace babban garin Ma'aloula da addinin kirista ya fi rinjaye, kwace wannan birni wani babban sakamako sojojin gwamnatin kasar suka samu a cikin wannan shekara a yankin dutse na al-Qalamoun da ke arewacin Damascus. Kuma har yanzu sojojin gwamnati na cigaba da farauta da zakulo ragowar dakarun da ke adawa da gwamnati a wuraren da ke kewayen garin Ma'aloula.
A bangaren lalata makamai masu guba, bisa shirin da kasar Sham ta gabatar, an ce, ban da kayayyakin kerar makamai masu guba da ke cikin na'urorin da ba a iya shiga ciki ba, ya kamata a kammala aikin jigilar da sauran makamai masu guba a ketare kafin ranar 13 ga wata, haka kuma kafin ranar 27 ga wata, za a lalata dukkan makamai masu guba tare da jigilar su zuwa ketare. Kakakin babban sakataren MDD ya bayyana a ran 14 ga wata cewa, ana nuna damuwa da jinkirin da ake samu wajen lalata makamai masu guba a halin yanzu. Tawagar wakilai ta MDD tana kokari cikin gaggawa domin tabbatar da jigilar makamai zuwa ketare kafin ranar 27 ga wata. In ba haka ba, to, za a kawo babbar illa ga matakin da aka amince ma na lalata dukkan makamai masu guba dake kasar Sham kafin ranar 30 ga watan Yuni. (Danladi)