in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Za a gudanar da babban zaben shugaban kasar Sham bisa lokacin da aka tsara
2014-04-09 11:02:29 cri

Ministan watsa labaru na kasar Sham Omran al-Zoubi ya bayyana a ran 8 ga wata cewa, za a gudanar da babban zaben kasar Sham na wannan shekara cikin lokacin da aka tsara.

Kafofin watsa labarum kasar sun ruwaito maganar Zoubi dake cewa, gwamnatin kasar za ta gudanar da shirye shiryen zaben kamar yadda da tsarin mulkin kasa ya tanada kuma bisa lokacin da aka tsara. Ya nuna cewa, gwamnatin kasar zata dukufa wajen ganin babban zaben shugaban kasar ya gudana yadda ya kamata, ba tare da amincewa ba da duk wani yunkurin wasu na hana wannan zabe ya gudana cikin kasar baki daya. Zoubi ya yi alkawarin gudanar da zabe cikin adalci kuma a fili. Ya kara da cewa, a karshen watan nan bangarorin da abin ya shafa za su iyar gabatar da 'yan takararsu.

A watan jiya, majalisar dokokin Sham ta zartas da wani kuduri, inda aka tabbatar da wasu sharudan da ake bukata daga wajen 'yan takara, wanda a ciki akwai matakin da ya shafi shekarun zama cikin kasar fiye da goma a jere, matakin da wasu bangarorin da ke adawa da gwamnati a ketare suka yi watsi da shi domin a cewarsu zai hana su shiga wannan zabe.

Haka kuma wasu 'yan adawa sun nuna shakkarsu, inda suka nuna cewa cikin halin yanzu gudanar da babban zabe, ba zai taimaka wa daidaita rikicin Sham a siyasance ba. Ban da wannan kuma, har yanzu ana cigaba da samun tashe tashen hankali a wasu yankunan kasar, lamarin da ya kasance wata babbar matsala wajen tabbatar da ikon kada kuri'a ga jama'ar da ke zama a wadannan wurare. (Danladi)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China