A wannan rana kuma, sojojin kasar Isra'ila sun tabbatar da cewa, an kai harin bom a yankin Tuddan Golan da ke dab da bakin iyakar Sham da Isra'ila, lamarin da ya raunata sojojin Isra'ila 4. Bayan fashewar bom din, sojojin Isra'ila sun jefa boma-bomai a wasu yankunan kasar Sham.
Tun bayan da aka fara yakin basasa a kasar Sham, ake ta yin musayar wuta da kai hare-hare da boma-bomai a wuraren da ke dab da bakin iyakar Sham da Isra'ila a yankin Tuddan Golan. Bisa labarun da muka samu daga kafofin watsa labaru na Isra'ila, an ce, jiragen saman yaki na Isra'ila sun jefa boma-bomai da yawa a wurare da dama a fadin kasar Sham. (Danladi)