Wang ya bayyana hakan ne a ranar Talata 25 ga watan nan a zaman babban taron MDD karo na 68, wanda ya mai da hankali ga tattaunawa kan halin jin kai a kasar ta Sham.
Mr. Wang Min ya bayyana cewa, warware takaddamar dake faruwa a siyasance, ta hanyar shawarwari, da daidaita bambance-banbancen ra'ayi, da amincewa juna ita ce hanya daya tilo ta wanzar da zaman lafiya. Ya kara da cewa ya kamata bangarorin kasar daban-daban, su sanya himma da gwazo a taron Geneva zagaye na biyu, su tsagaita bude wuta, tare da dakatar da amfani da karfin tuwo ba tare da bata lokaci ba.
Kazalika wakilin na kasar Sin ya kara da cewa, tun barkewar rikicin siyasar kasar, Sin ke iyakacin kokarin kyautata halin jin kai a kasar. Kuma za ta ci gaba da baiwa jama'a da 'yan gudun hijira dake kasashen ketare taimako yadda ya kamata.
Ya ce a matsayinta na wakiliya a kwamitin sulhu na MDD, kuma kasar dake sauke nauyin dangantakar kasa da kasa dake wuyanta, Sin za ta gabatar da jerin shawarwari kan yadda za a warware rikicin na Sham a siyasance. Bugu da kari Sin za ta ci gaba da goyon bayan matakan siyasar kasar, tare kuma da mara baya ga kokarin da babban magatakardar MDD Ban Ki-Moon, da wakilin musamman na kungiyar kawancen kasashen Larabawa da MDD Lakhdar Brahimi ke yi, baya ga gudunmawarta ga batun warware rikicin kasar ta Sham cikin dogon lokaci a kuma dukkan fannoni. (Amina)