in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin za ta yi kokarin raya tattalin arzikinta, in ji firaministan kasar Sin
2014-06-10 20:56:18 cri
Firaministan kasar Sin Mr Li Keqiang ya yi jawabi a gun tarukan manyan cibiyoyin nazarin kimiyya da fasaha na kasar Sin a yau Talata 10 ga wata, inda ya yi bayyani kan halin da tattalin arziki Sin ke ciki, ya ce, tun farkon wannan shekara da muke ciki, ake fuskantar mawuyacin hali a gida da kuma waje, amma a kokarin daukacin Sinawa, tattalin arzikin Sin ya samu bunkasuwa yadda ya kamata,inda wasu muhimman ma'aunai suka kai matsayin da ya dace, kuma kyautatuwar ta amfana, makomar kasuwanni da sauran alkaluma na cikin hali mai kyau.

Li Keqiang ya jaddada cewa, yadda tattalin arzkin Sin ke ci gaba da samun matsakaicin bunkasuwa ko cikin sauri ya dogaro da yadda ake gudanar da ayyukan kirkire-kirkire musamman ma hada ayyuka kirkire-kirkire na fannin kimiya da tsare-tsare tare, ta yadda za su samu ci gaba baki daya. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China