
Firaministan kasar Sin Li Keqiang ya halarci bikin bude taron majalisar nazarin fasahohi ta kasa da kasa na shekarar 2014 a safiyar yau Talata 27 ga wata, tare da ba da jawabi. Inda ya nuna cewa, ya kamata, a bunkasa kimiyya da fasaha tare cikin hadin kai. Kasashe daban-daban a duniya suna yin amfani da hanyoyi daban-daban wajen yin musayar fasahohin kimiyya da fasaha. Sin kuma na fatan kara hadin kai da yin musayar ra'ayi tsakanin kasa da kasa a fannoni kimiyya, fasaha, kwararru, har ma da goyon bayan kafa tsarin samun ilmi ba tare da wata rufa-rufa ba karkashin wani tsarin bayar da taimakon kudi, da sa kaimi ga bunkasuwar sha'anin kimiya da fasaha na Sin har ma na duniya gaba daya. (Amina)