in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Firaministan Sin ya gana da babban sakataren MDD a birnin Beijing
2014-05-20 10:59:35 cri

Firaministan kasar Sin Li Keqiang, wanda ya gana da babban sakataren MDD Ban Ki-moon a ranar Litinin, ya furta goyon bayan rawar da MDD ke takawa ta daukar matakai a kan harkokin da suka shafi yankuna da na duniya baki daya.

A yayin da yake magana a kan ayyukan MDD na ci gaba a bayan shekara ta 2015, Li ya lura da kalamai guda ukku, wadanda suka hada da bunkasa, hakuri da juna da hadin gwiwa.

Firaministan na Sin, ya ce, ya kamata batutuwan ajandar ci gaban ta hada da rage tasirin talauci, yin la'akari da bukatun kasashen da suka ci gaba da kuma bukatun kasashe masu tasowa, da kuma hada hannun duniya baki daya wajen aiki da tsarin gaskiya, da tabbatar da baiwa kowa hakkin sa, da kuma tunkarar zalaka a daukacin al'amurra.

Li ya kuma bayyana matsayin kasar Sin, a game da canjin yanayi, inda ya jaddada cewar, Sin ta damu ainun a game da lamurran yanayi da ci gaba, a inda ya bukaci da a aiwatar da tsarin hakkoki daban daban da suka wajaba a wanan fannin

Firaministan na Sin ya ce, kasar Sin a shirye take ta yi aiki kafada-da kafada da MDD a wajen yaki da dumamar yanayi tare da zaburar da ci gaban da ya dace.

A jawabinsa, babban sakataren MDD Ban Ki-moon ya yaba da gudumuwar da kasar Sin take bayarwa ga ayyukan MDD a fannoni daban daban, a inda ya lura da cewar, ziyarar da firaminstan kasar Sin ya kai Afrika a kwanan nan za ta taimaka kwarai wajen zaburar da ci gaban nahiyar.

Ban ya kara da cewa, MDD ta yaba matuka da taimakon da kasar Sin ta baiwa Afrika da kuma fafutukar da Sin ke yi wajen yaki da gurbatar yanayi, Ban ya kara da cewa, MDD a shirye take ta yi aiki tare da kasar Sin domin samar da ajandar ci gaba a bayan shekara ta 2015. (Suwaiba)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China