in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Firaministan Sin ya gana da shugaban dandalin tattaunawar tattalin arzikin duniya
2014-05-28 20:43:39 cri
A yammacin yau Laraba 28 ga wata ne, firaministan kasar Sin Li Keqiang ya gana da shugaban dandalin tattaunawar tattalin arzikin duniya (WEF), Klaus Schwab a birnin Beijing na Sin.

Firaminista Li ya bayyana cewa, yanzu tattalin arzikin duniya yana farfadowa kuma ana fama da matsaloli iri iri. Don haka kamata ya yi kasashe masu sukuni da kasashen da tattalin arzikinsu ke bunkasa su taimakawa juna, domin tinkarar babban kalubalen tattalin arziki a duniya tare, da zummar sa kaimi ga farfadowar tattalin arzikin duniya yadda ya kamata.

A nasa bangare, Klaus Schwab ya bayyana cewa, jawabin da firaminista Li ya yi a wajen taron kolin tattalin arzikin duniya kan Afirka a kwanan baya, ya kara wa mutane kwarin gwiwa sosai. Wannan ya sa ake yaba masa sosai. Hakan ya kara wa jama'ar kasashen Afirka kwarin gwiwar tinkarar kalubale. Yin kwaskwarima da bunkasuwar kasar Sin za su taimaka sosai wajen sa kaimi ga farfado da kuma bunkasa tattalin arzikin duniya. Dandalin WEF ya nuna godiyarsa ga kasar Sin, da fatan zai karfafa hadin gwiwa tsakaninsa da Sin, domin kara taka rawar a zo a gani tare da Sin wajen kyautata ci gaban tattalin arzikin duniya, da sa kaimi ga raya tattalin arzikin duniya baki daya. (Fatima Liu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China